A cikin shirin za a ji cewa: Mataimakiyar shugaban Amirka Kamala Harris ta isa kasar Ghana a matakin farko na ziyarar da ta fara a wasu kasashen Afirka, Ukraine ta bukaci kwamitin sulhu na MDD da ya yi zaman gaggawa kan shirin Rasha na aike da makaman nukiliya Belarus.