A Najeriya kungiyar IPOB mai neman kafa kasar Biafra ta janya dokar da ta kakabawa al'ummar yankin kudu maso gabashin Najeriya. A Jamhuriyar Nijar kuwa za ku ji cewa, wata takaddama ta kunno kai tsakanin ministan ilmi mai zurfi da ma'aikatan jami'o'i na kasar.