1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin zabukan gama gari a Burkina Faso

Lateefa Mustapha JaafarNovember 27, 2015

Al'ummar kasar Burkina Faso na shirin gudanar da babban zabe a ranar 29 ga watan Nuwamba, inda za su zabi shugaban kasa da kuma 'yan majalisun dokoki.

https://p.dw.com/p/1HDk4
Hoto: imago/Xinhua Afrika

A yanzu dai za su sake zaben shugaban kasa wanda kuma suke fatan zai tabbatar da dorewar mulkin demokaradiyya a kasar. Ko da yake bayan saukar tsohon Shugaba Compaore sojoji sun yi wani dan kwarya-kwaryan juyin mulki na tsahon mako guda, cikin watan Satumbar da ya gabata, sai dai sun sake mayar da mulkin ga gwamnatin rikon kwaryar kasar. Fousseni Nakolemda, matashi ne da ke karatun gaba da sakandare wanda kuma ke da kimanin shekaru 27 a duniya ya ce wannan shi ne karo na farko da zai kada kuri'arsa kuma ya na zumudin zuwan wannan ranara.

Burkina Faso Präsidentschaftswahl Fousseni Nakolemda
Hoto: DW/K. Gänsler

"Bayan shekaru 27 na mulkin gwamnatin kama karya ta Shugaba Compaoré, yanzu dama ce a garemu na mu sauya al'amura. Ya zama tilas mu hade kai a wajen zabe, mu hada kai mu zabi duk mutumin ko kuma duk jam'iyyar da za ta taimaka wa matasa. Muna son mu yi nesa da wannan siyasa ta rishin gaskiya sai yawan alkawurra ba cikawa, kuma da karshe gidan jiya noman goge kenan a gaskiya muna son sauyi."

A ganin matasan kasar dai daga cikin 'yan takara 14 da suke son zama shugaban kasa babu wanda ke yin batun matasa a yayin gangamin yakin neman zabensa, dukannunsu na cewa za su yaki cin hanci da almundahana da kudaden jama'a ne kawai, bayan kuma kusan kaso 65 na al'ummar kasar matasa ne 'yan shekaru 25 ko ma kasa da haka. A cewar shugaban gidauniyar Hanns-Seidel da ke da alaka da jam'iyayar CSU ta nan Jamus a Ouagadougou babban birnin kasar ta Burkina Faso Ralf Wittek ba lallai ne 'yan takara su cika alkawuran da suke dauka ba.

"Zai yi wahala su cika alkawura da suke yi wadanda basu da karshe. Akwai wasu 'yan takara da ba a rasa ba, misali Jean-Baptiste Natama wanda zan iya cewa zai yi matukar kokari wajen kawo sauyi, sai dai ba shi da wannan damar saboda ba shi da madafa. Madafa a nan itace kudi wato masu gidan rana sune kullum a kan gaba."

Hamidou Zoetaba
Hoto: DW

Za dai a iya cewa 'yan takara biyu ne ke da kudin kuma dukkansu na da alaka da tshohon shugaban kasar ta Burkina faso Blaise Compaore kasancewar dukkansu sun yi aiki da shi. Zéphirin Diabré mai kimanin shekaru 56 a duniya na jam'iyyar UPC ya yi minista a karkashin Compaoré kafin ya koma jam'iyyar adawa, yayin da Roch Marc Christian Kaboré mai shekaru 58 na jam'iyyar CDU da ke mulki a wancan lokaci ya kasance Firaminista.