Shugaban kasa kuma minista a Burkina Faso
January 13, 2016Sabon shugaban kasar Burkina Faso Roch Kabore ya bayyana kansa a matsayin ministan tsaro a kasar Burkina Faso a ranar Laraban nan sannan ya nada kansa a matsayin ministan da ke lura da harkokin tsaffin sojojin kasar, wannan na zuwa ne cikin sabuwar majalisar ministocin kasar da ya bayyana cikin wata sanarwa da ta fita a rediyon kasar ta Burkina Faso.
Majalisar ministocin ta hadar da 'yan jarida guda biyu da suka hadar da Alpha Barry na gidan rediyon Omega FM wanda aka ba shi ministan harkokin kassahen wajeda Remi Dandjinou na wani gidan talabijin mai zaman kansa a kasar ta Burkina Faso ministan kula da ma'aikatar sadarwa da harkokin majalisa.
Wannan nadi dai na zuwa ne kasa da mako guda bayan da shugaba Kabore ya bayyana Paul Kaba Thieba a matsayin Firaminista.