SiyasaAfirka
Shugaban Benin na kokarin lashe zabe a karo na biyu
April 12, 2021Talla
Tun kafin hukumar zaben kasar ta fitar da kammalallen sakamakon zabe, masu adawa da shugaban sun fara zargin sa da murdiya ta hanyar kuntata wa jagororin adawa.
Shugaban na Benin dai na fuskantar wasu 'yan takara daga bangaren adawa guda biyu da ake ganin duk yadda za ta kaya ba za su iya kayar da shi ba. Sai dai a gabanin zaben an zargi Shugaba Talon da amfani da hukumomin kasar wurin tsame sunayen jiga-jigan adawar da ya ke tunanin za su kawo masa tarnaki a zaben.
A shekara ta 2016 ne dai aka fara zaben Shugaba Talon a matsayin shugaban kasar ta Jamhuriyar Benin, kuma a cikin kasar wasu na ganin ya taimaka wurin habbakar tattalin arzikin kasa.