Nijar: Tayin gwamnatin hadin kan kasa
March 23, 2016Talla
Shugaba Mahamadou Issoufou da aka sake zabe a jamhuriyar Nijar a zangon wa'adi na biyu bayan zaben da ke cike da cece-ku-ce a ranar Laraban nan ya yi tayi na gwamnatin hadin kan kasa tare da 'yan adawa, wadanda suka kaurace wa zaben da aka yi zagaye na biyu a karshen makon da ya gabata.
A wata zantawa da shugaban ya yi da kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya bayyana cewar a shirye yake ya yi gwamnati ta hadin kan kasa tare da 'yan adawar dan a tinkari matsaloli da al'ummar kasar ta Nijar ke fiskanta.