1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Shugaban WHO ya tsallake rijiya da baya a harin Isra'ila

December 26, 2024

Mista Ghebreyesus da tawagarsa suna filin jirgin Yemen ne a yayin da harin Isra'ila a wurin ya kusa rutsawa da su.

https://p.dw.com/p/4obRN
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Ghebreyesus
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Ghebreyesus Hoto: Lian Yi/Xinhua/picture alliance

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesusya tsallake rijiya da baya yayin wani hari da Isra'ila ta kaddamar kan filin jirgin Yamen a ranar Alhamis.

Mista Ghebreyesus da kuma tawagarsa sun kai ziyarar aiki ne a hukumance zuwa Yamen kuma shugaban na WHO ya ce sun kusa tashi kenan daga filin jirgin babban birnin Yemen Sana’a a yayin da harin ya auku.

Masar ta yi nasarar kawar da cutar zazzabin cizon sauro: WHO

Isra'ila ta kaddamar da wasu jerin hare-hare  kan filin jirgin Yemen kwana daya bayan mayakan Huthi sun farmata.

Luguden wutan da aka yi kan filin jirgi da muhimman wuraren soji da na makamashi ya biyo bayan tsamin dangantaka ne tsakanin Isra'ila da Huti da ke samun goyon bayan Iran.

An kuma kaddamar da wasu hare-haren a birnin Hodeida kamar yadda wani shaida da kuma tashar talabijin ta Al-Masirah suka ruwaito.

WHO: Za a iya kawar da corona a 2022

Sau shida Isra'ilar ta kai hari kan filin jirgin na babban birnin Yemen da ke karkashin mayakan na Huthi kuma daya daga cikin mutanen tawagar ta WHO ya samu rauni.