1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumar tarayyar Turai ta sanya sabon burin kare muhalli

Mohammad Nasiru Awal USU
September 16, 2020

A jawabinta na farko kan halin da kungiyar EU ke ciki shugabar hukumar EU, Ursula von der Leyen ta ce dole EU ta kara yawan burin rage fidda hayaki.

https://p.dw.com/p/3iYe4
Ursula von der Leyen's Rede zur Lage der EU
Hoto: Reuters/Y. Herman

Shugabar hukumar tarayyar Turai ta EU, Ursula von der Leyen ta ce hukumar za ta rage yawan gurbatacciyar iska ta CO2 a tsakanin kasashen kungiyar EU zuwa kashi 55 cikin 100 kafin nan da shekarar 2030.

Von der Leyen ta bayyana wannan sabon kuduri ne a jawabinta na farko kan halin da kungiyar EU ke ciki a gaban zauren taron wakilan Turai da ke gudana daga 14 ga watan nan na Satumba zuwa 17 ga wata a birnin Brussels.

"Hukumar tarayyar Turai na ba da shawarar kara yawan burinmu game da rage fidda gurbatacciyar iska mai dumama yanayi ya zuwa akalla kashi 55 cikiin 100 kafin shekara ta 2030. Kashi 37 cikin 100 na sabbin ayyukan EU za su tafi ne wajen samar da makamashi da ba ya gurbata muhalli."