1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Soja: Isaac Zida ne zai zama firaminista

November 19, 2014

Al'ummar Burkina Faso na jiran nadin sabon Firaminista na rikon Kwarya. Alamu na nunawa cewa shugaban mulkin soja Isaac Zida ne za a dora kan wannan mukami

https://p.dw.com/p/1DpW3
Hoto: Reuters/J. Penney

Tuni dai wani babban soja na kusa da Kanar Isaac Zida ya sanar cewa sabon shugaban riko na Burkina Fasi Michel Kafando, zai nada Isaac Zida ne a mukamin na firaminista domin mutunta wata yarjejeniya da suka cimma tare da fararar hullar kasar.

Shi dai wannan soja ya ce sun tattauna kan za'a basu mukamin firaminista, kuma kowa ya amince da hakan. Ya kuma kara da cewa sojojin sun amince su bar shiga cikin majalisa ta rikon kwarya, amma zasu kasance cikin gwamnati.

A ranar Jumma'a ce dai Shugaban na mulkin soja Kanar Isaac Zida zai mika mulkin a hannun sabon shugaban na rikon kwarya yayin wani kwarya-kwaryar biki da za'a shiyra kan hakan a birnin na Ouagadougou.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe