1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojin Amirka sun kai hari kan Al-Shabaab

Aliyu Muhammad Waziri
July 5, 2017

Rundunar sojin Amirka ta ce dakarunta sun kai jerin hare-hare kan mayakan kungiyar nan ta Al-Shabaab a wani yanki da ke da tazarar kilomita kusan 300 yamma da Mogadishu, babban birnin kasar Somaliya.

https://p.dw.com/p/2g0J8
Somalia Al-Shabaab Kämpfer
Hoto: picture alliance/AP Photo/F. A. Warsameh

A wata sanarwa da rundunar wadda ke aikinta a nahiyar Afirka ta fitar, ta ce nan gaba za ta yi karin haske kan sakamakon wannan hari da aka kai dazu musamman ma dai yawan mayakan da aka samu nasarar hallakawa. Rundunar dai ta daura yaki ne da 'yan kungiyar ta al-Shabaab da ke da alaka da kungiyar nan ta al-Qa'ida a wani mataki na ganin ta kawar da masu tsaurin kishin addini da ke wannan kasa da nufin kawo karshen tada kayar bayan da suke yi.