1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sojin Mali sun cafke wani jagoran kungiyar IS a yankin Sahel

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
January 5, 2025

Wadanda aka kama sun hada da Mahamad Ould Erkehile da aka fi sani da Abu Rakia, sai kuma Abu Hash da ke zama jagora a IS a Sahel.

https://p.dw.com/p/4opMH
Shugaban mulkin sojin Mali Assimi Goita
Hoto: OUSMANE MAKAVELI/AFP/Getty Images

Rundunar sojin Mali ta sanar da cewa dakarunta sun samu nasarar halaka 'yan ta'adda da dama a arewacin kasar, sannan kuma suka cafke wasu mutane biyu, cikinsu har da jagoran wani tsagi na kungiyar ta'addanci ta IS a yankin Sahel.

Karin bayani:Mali ta shafe sunan Faransa a titunanta

Sanarwar da rundunar sojin ta fitar ta ce wadanda aka kama din sun hada da Mahamad Ould Erkehile da aka fi sani da Abu Rakia, sai kuma Abu Hash da ke zama jagora a IS din, wanda ya kitsa hare-haren ta'addancin da aka rinka kai wa garuruwan Menaka da Gao, har da wadanda aka kai wa sojojin kasar.

Karin bayani:ECOWAS ta sahale wa Nijar da Mali da Burkina Faso fita daga kungiyar

Tuni dai Mali ta katse hulda da uwargijiyarta Faransa sannan ta kulla alaka da Rasha, domin ta taimaka mata wajen yaki da ta'addanci, wanda take fama da shi daga kungiyoyi masu alaka da Al-Qaeda da kuma IS tun a shekarar 2012.