Sojoji sun yi garkuwa da shugaban kasar Burkina Faso
September 16, 2015Rundunar da ke kare fadar shugaban kasa a Burkina Faso ta katse taron majalisar zartaswar kasar tare da tsare manyan jami'an gwamnati da suka hada da Shugaban wucin gadi Michel Kafando da Firaminista Yacouba Isaac Zida gami da ministoci. Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito wasu majiyoyi da ke tabbatar da labarin.
Wani babban jami'an soja ya ce babu wasu tambayoyi da aka yi wa manyan jami'an gwamnatin da wasu sosjoji suka tsare da suka hada da shugaban kasa da firaminista. Kawo yanzu babu cikekken labari kan abin da ke faruwa a kasar da ke yankin yammacin Afirka. A watan gobe na Oktoba aka tsara zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki domin mayar da kasar ta Burkina Faso tafarkin demokaradiyya bayan bore da ya kawo karshen gwamnatin Shugaba Blaise Compaore ta shekaru 27.