Sojoji sun yi harbe-harbe a Burkina Faso
January 23, 2022Rahotannin da ke fitowa daga Ouagadougou babban birnin kasar Burkina Faso, na cewa an ji rugugin muggan makamai a birnin da kewaye, inda fargaba ta lullube kasar a kan yiwuwar kifar da gwamnatin Shugaba Roch Marc Christian Kabore.
Da fari dai an yi zaton sojoji ne ke furjanye wa shugabanninsu, inda kafar watsa labaran RTB a kasar, ta siffanta lamarin da rashin gamsuwa daga sojojin Burkina Faso.
Hukumomi dai sun tabbatar da harbe-harebn daga barikin soji da ke a Ouagadouguo, sai dai sun kore batun juyin mulki.
Babu dai labarin kame Shugaba Roch Marc Christian Kabore ya zuwa yanzu, kamar yadda su ma jagororin sojin kasar suka fada.
A ranar Asabar ma 'yan kasar ta Burkina Faso sun yi zanga-zangar neman gwamnati ta kawo karshen rashin tsaro da ake fama ada shi daga hare-haren masu ikirarin jihadi.