1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojoji sun yi juyin mulki a Burkina Faso

Umaru AliyuSeptember 18, 2015

Mafi yawan jaridun Jamus sun maida hankalin sharhunansu ne kan juyin mulkin da siojoji suka aiwatar da kasar Burkina Faso ranar Larabar da ta wuce.

https://p.dw.com/p/1GYe1
Burkina Faso Ouagadougou Putsch
Hoto: Reuters/J. Penney

Jaridar Süddeutsche Zeitung ta fara ne da cewar da ma gwamnatin da akai wa juyin mulkin, gamnati ce dake rikon kwarya kafin zabe na gaba a kasar ta Burkina Faso. Ranar Laraba sojoji masu tsaron fadar shugaban kasa suka kutsa majalisar dokoki, inda suka tsare shugaban wucin gadi, Michel Kafando da yan majalisar ministocinsa. Nan da nan kuma sojojin karkashin Janar Gilbert Diendere, suka sanar da rufe iyakoki da dakatar da suhurin jiragen sama, ko da shike sun yi alkawarin gudanar da zabe cikin gaggawa....Ita ma jaridar Neue Zürcher Zeitung ta ce sojojin sun karbe mulki a Burkina Faso, inda suka kawo karshen zanga-zangar kungiyoyi dake fafitikar tabbatar da democradiya a wannan kasa. Wannan juyin mulki, inji jaridar, ya zo ne shekara guda bayan juyin juya halin democradiya a kasar, kuma wata guda kafin zaben da aka shirya a cikinta. Rahotanni sun una cewar sojojin da suka yi juyin mulkin, makusanta ne ga shugaban kasar da aka kawar a bara, Blaise Compaore, saboda ganin cewar shugaban juyin muljin, Michel Diendere, tsohon hafsan hafsoshi n e na zamanin Compaore... A nata sharhin, jaridar Tagesspiegel maida hankali ne ga ra'ayoyin kungiyoyi da kasashen duniya tattare da juyin mulkin na Burkina Faso. Jaridar tace cikin wadanda suka yi Allah wadai da wannan mataki, har da ministan harkokin wajen Jamus, Frank-Walter Steinmeier, da Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar kasashen Afirka Ta Yamma, wato ECOWAS. Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon yayi kira ga wadanda suka aiwatar da juyin mulkin su gaggauta sakin jami'an tsohuwar gwamnatin da suka tsare, ciki har da shugaban kasa, Michel Kafando da Pirayim minista Isaac Zida. Cherif Sy da kungiyar nman hakkin jama'a ta Balai Citoyen suma dai sun nemi yan Burkina Faso su nuna adawarsu kan tituna da mulkin na soja.

A Jamhuriyar Democradiyyar Kwango, an shirya gudanar da zabe a watan Nuamba na shekara ta 2016. A kan haka ne jaridar Tageszeitung tayi sharhinta, inda tace ana kara ganin cewar gudanar da zabe mai tsabta ba abu ne mai yiwuwa ba. Jaridar Tageszeitung tace wata da watanni kenan ana ci gaba da samun sabani kan yadda za a tafiyar da zaben, musamman bayan da cikin watan Janairu, shugaban kasa, Joseph Kabila yace za'a sake tsarin rajistar masu zabe, kuma shi kansa yana da shirin yiwa kundin tsarin mulkink asar ta Kwango gyaran fuska, domin tsayawa takara karo na ukku. Bayan da jam'iyun adawa suka amince da sabunta rajistar masu zaben, yanzu kuma sun zargi gwamnatin Kabila da laifin amfani da kudin rajistar da aka yi amfani dashi tun shekara ta 2011, a zaben na shekara mai zuwa.

Yayin da dubban 'yan gudun hijira suka mamaye nahiyar Turai, jaridar Süddeutsche Zeitung a wani sharhi da tayi, tace ana neman mantawa da dubban 'yan gudun hijira dake shawagi, suna neman mafaka a Afirka dake yake-yake na kasashensu. Jaridar tace mafi yawan wadannan 'yan gudun hijira ana samunsu ne a Afirka ta Gabas, inda Kenya take zama kasar da tafi karbar yan gudun hijiran. Jaridr tace yayin da ake damuwa da makomar dimbin mutanen dake kaura daga kasasahe kamar Siriya ko Irak ko Afghanistan zuwa Turai, kasashe kamar Somaliya su ma dai suna cikin wani mummunan hali, ga rikici a Sudan ta kudu, yayin da al'ummar Sudan Ta Arewa su ma basu tsira ba daga mulkin kama karya na shugabanninsu. Ana iya ganin yadda duniya ta manta da yake-yake a Afirka, idan aka duba rashin kula da ake baiwa sansanin yan gudun hijira mafi girma a duniya, ato sansanin Dadaab dake Kenya, mai dauke da yan gudun hijira 300.000 a cikinsa.

Symbolbild Frauen Vergewaltigung Not Hunger Armut in Somalia
Hoto: Oli Scarff/Getty Images

Msu sauraronmu da wannan sharhi na jaridar Süddeutsche Zeitung za mu dakata a shirin na yau, Yusuf gareka.))