Sojojin Amirka sun kaddamar da farmaki a Somaliya
September 2, 2014Talla
Ma'aikatar tsaron Amirka ta Pentagon ta tabbatar da cewa, a wannan Litinin da ta gabata sojojin kasar sun kaddamar da wani farmaki a cikin Somaliya, kan mayakan al-Shebaab.
Babu karin bayani bisa halin da ake ciki, amma haka ya biyo bayan wani hari da 'yan al-Shebaab da ke da alaka da al-Qaeda suka kai kan wani sansanin jami'an tsaro.
Cikin watannin da suka gabata dakarun kasar ta Somaliya da tallafin na kasashen Afirka sun kwace mafi yawan yankunan da suka rage a hannun al-Shebaab mai kaifin kishin addinin Islama.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu