1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Faransa sun kori 'yan jihadi a Mali

Salissou Boukari
May 1, 2017

Dakarun sojojin kasar Faransa da ke ayyukan tsaro a yankin Sahel sun fatattaki mayakan jihadi da dama tare da kame wasu daga cikinsu a iyakar Burkina Faso da Mali.

https://p.dw.com/p/2cAUd
Symbolbild Afrika Sicherheit im Sahel
Jirgi mai saukar ungulu na sojojin kasar Faransa a SahelHoto: Pascal Guyot/AFP/Getty Images

Rundunar sojojin kasar ta Faransa ce dai ta sanar da wannan labari da yammacin ranar Lahadi, inda ta ce tun dai daga ranar Asabar ce da ta gabata, sojojin na Faransa na Barkhane suka ayyana wani samame wanda hakan ya ba su damar fatattakar da 'yan jihadin kusan 20 a yankin gandun dajin Foulsare da ke kusa da iyakar kasar ta Mali da Burkina Faso.

Da farko dai jiragen yakin kasar ta Faransa sanfarin Mirage 2000 ne suka soma da kai hare-hare ta sama a wasu wurare da ake zaton maboyar 'yan jihadin ce da kuma makamman su sannan daga bisani wasu jirage masu saukar ungulu guda biyu suka samar da tsaro a yankin wanda hakan ya bada dama ga sojoji na musamman na kasar Faransa su sauka cikin gandun dajin domin yakar 'yan jihadin.