1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Macron ya sanar da ficewar sojin Turai daga Mali

Abdourahamane Hassane
February 17, 2022

Faransa da kawayenta na Turai za su fara janye sojojinsu daga Mali nan da watanni shida masu zuwa, biyo bayan tsamin danganta da mahukuntan Bamako.

https://p.dw.com/p/47B4d
Frankreich |  Emmanuel Macron mit Senegals Präsident Sall und Ghanas Präsident Akufo-Addo
Akufo Ado na Ghana, Macky Sall na Senegal da Emmanuel Macron na FaransaHoto: Ludovic Marin/AFP/Getty Images

 Kimanin sojojin 4600 na Faransa ke a yankin Sahel daga cikinsu 2400 na jibge a Mali. Faransar ta bayyana sanarwar janye sojojin nata ne bayan tsawon shekaru tara na yaki da ta'addanci a kasar.

Duk da cewar Faransar ta janye daga Malin amma ta ce za ta ci gaba da kasancewa a cikin kasashen yankin Sahel da na Gulf na Guinea. A cikin jawabin da yayi shugaban Faransar Emmanuel Macron ya ce da sannu a hankali a cikin watanni hudu zuwa shida za a janye sojojin na Faransa da na sauran kasashen Turai da ke a cikin rudunonin soji na Takuba da kuma Barkhane saboda rashin fahimtar da ke tsakaninsu da Malin.

"Ba zamu iya ci gaba da yin aiki ba tare da hukumomin da manufofinmu sun bambanta, ra'ayoyinmu suka yi hannun riga abinda mu ke fuskanta yau ke nan a Mali. Kuma yaki da ta'addanci ba za a kafe da shi ba a dore a kan mulki har abadan abada".

Französischen Marine-Spezialeinheiten bildet in Mali aus
Sojin Faransa da ke yaki da 'yan tawaye a MaliHoto: Thomas Coex/AFP/Getty Images

Kanada da sauran kasashen Turai da ke a aiki tare da Faransar a Sahel wadanda ke da sojoji a cikin rundunonin Takuba da Barkhane sun ce yanayin da ake ciki na cikas din da Malin take kawowa, ba zai bari ba su ci gaba da jagorancin aikin na yaki da ta'addanci ba a kasar, bayan da Malin ta dauko sojojin haya na Rasha Wagner domin kula da aikin tsaron abinda ke nufin cewar su ma sauran kasashe da ke aiki tare a Faransa za su janye dakarunsu daga Malin. Josephe Borrell shi ne jagoran diplomasiya na kungiyar EU:

"A yanzu abin da ke da mahimmanci shi ne me za mu yi, mu kasashen Turai, da farko za mu aika tawaga zuwa Mali domin tattaunawa da hukumomi don sannin ko jami'anmu da ke can suna ba da horon soji ko za su ci gaba da aikin ko a'a, sai cikin kwanaki na gaba a samu amsar wannan tambaya".

Ministan harkokin waje ta Jamus ta ce ba ta da tabbas kan cewar ko za su tsawaita wa'adin rundunar sojojinsu a Mali wadda a cikin watan Mayu da ke tafe majalisar dokokin kasar ta Bundestag za ta bayyana matsayinta a game da wannan batu kan cewa ko sojojin Jamus za su ci gaba da kasancewa a Mali ko akasin haka.

Afrika Militär Missionen von Barkhane in Mali
Rundunar Barkhane a MaliHoto: Etat-major des armées / France

Faransar za ta rufe sansanonin rundunonin sojojin da ke a Gossi da Menaka a kuma Gao da ke a rewacin kasar a cikin watannin hudu zuwa shida wadanda ke aiki a cikin rundunar Takuba wadanda za a mayar da su a Nijar. Shugaban kasar Senegal Macky Sall ya ce ya gamsu da yadda kasashen Turan za su ci gaba da yaki da ta'adanci a Sahel duk da cewar sun janye daga Mali.

Akwai sojoji kusan dubu 25 na kasashen da ke yaki da taaddanci a Sahel daga cikinsu kimanin 4300 na Faransa a rundunonin Takuba da Barkane ban da na rundunar kiyaye zaman lafiya ta MDD Minusma.

A shekara ta 2013 Malin ta yi kira ga Faransar da ta ceceta daga hannun masu Jihadi da suka kwace yankin arewacin kasar. To amma a baya-baya nan an dada samun rashin jituwa tsakanin Paros da Bamako saboda karan tsaye da hukumomin sojojin na Malin suka yi na kin bayyana jadawalin sabon zabe domin mika mulki hannu farar hula bayan juyin mulki har biyu da aka yi a kasar a cikin kankane lokaci.