1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Nijar da Faransa sun kai hari a kusa da Mali

October 30, 2022

Dakarun gwamnatin kasar Nijar da na Faransa, sun kai wasu samame na hadin gwiwa a kan mayakan tarzoma da ke ikrarin jihadi a iyakar Nijar din da makwabciyarta Mali.

https://p.dw.com/p/4Iqmy
Hoto: LUC GNAGO/Reuters

Samamen da suka kai 15, dakarun sun kai su ne a tsakanin watan Yuli zuwa Oktoba da muke ciki, kamar yadda rundunar sojin Jamhuriyar Nijar ta tabbatar.

A makon jiya ne dai aka sake fasalta sintirin na hadin gwiwa tsakanin mayakan na hadin gwiwa, bayan wata ganawa tsakanin babban hafsa hafsoshin kasar Janar Salifou Modi da sojojin Faransa

Dakarun sun yi nasarar kama wasu ake zargi 'yan ta'adda su 30 da tarin makamai da na'urorin sadarwa, sannan an lalata ababen hawa da suke amfani da su.

Sai dai a ranar Asabar na makon jiya akalla 11 sun mutu a wani hari da 'yan bindiga suka kai a iyakar kasar da Mali.