Sojojin Somaliya sun shiga garin Kismayu
October 1, 2012A wannan Litinin an girke ɗaruruwan sojojin gwamnatin Somaliya da mayaƙan sojojin sa kai dake mara musu baya a tsakiyar garin Kismayu dake zama sansanin sojojin sa kan ƙungiyar Al-Shabaab. Mohamud Farah kakakin rundunar sojin gwamnati a yankunan kudancin Juba ya faɗa wa kamfanin dillancin labarun Reuters cewa an aike da dakaru 450 domin sintiri a garin, sannan za a tsugunar da su a shelkwatar 'yan sanda. Da farko dai an jiyo kakakin sojin na cewa dakarun tarayyar Afirka da na gwamnatin Somaliya ba za su yi gaggawar shiga garin ba a daidai lokacin da ake fama da zaman ɗarɗar game da hare haren ɗaukar fansa da suka addabi garin mai tashar jirgin ruwa. Kawo yanzu ba a sani ba ko dakarun ƙasar Kenya dake faɗa ƙarƙashin tutar rundunar kiyaye zaman lafiya ta ƙungiyar tarayyar Afirka, su ma sun shiga tsakiyar garin. A ranar Juma'a mayaƙan al-Shabaab suka tsere daga Kismayu biyo bayan wani farmakin ba zata da sojojin ruwa da na sama da kuma na ƙasa suka kai.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Saleh Umar Saleh