1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Somaliya sun ƙwace garin Baidoa

February 22, 2012

Bisa tallafin takwarorinsu na Habasha, sojojin Somaliya sun mayar da birnin Baidoa ƙarƙashin ikonsu, sakamakon fatattakar 'yan al-Shabab da suka yi daga birnin.

https://p.dw.com/p/147pv
Kenyan army soldiers patrol near their base in Tabda, inside Somalia Monday, Feb. 20, 2012. Kenya's military has been fighting inside Somalia in an ongoing offensive against militant group al-Shabab since October, when Somali gunmen carried out several kidnappings in Kenya. (Foto:Ben Curtis/AP/dapd)
Sojojin ƙaasshen Afika sun saba tallafa wa na Somaliya.Hoto: AP

Dakarun gwamnatin riƙon ƙwaryar Somaliya sun yi nasarar fatattakar mayaƙan sa kai na ƙungiyar Al-shabab daga cibiyarsu da ke garin Baidoa. Wannan dai shi ne karon na farko da sojojin na Somliya, bisa tallafin takwarorinsu na Habasha, suka taɓuka wani abin kirki a watannin baya-bayanan a sa toka sa katsi da suke yi da masu tsananin kishin addinin musuluncin. Sai dai kuma shugabannin ƙungiyar al-Shabab sun nunar da cewa sun fice daga birnin na Baidoa ne don raɗin kansu. Ba don komai ba kuwa, sai don ɗaura sabuwar ɗamarar ƙalubalantar waɗanda suka danganta da maƙiya Allah.

wannan dai ya zo ne a daidai lokacin da kwamitin sulhu na MDD ya amince da ƙara sojojin kiyaye zaman lafiya a ƙasar ta Somaliya i zuwa dakaru sama da dubu 17. ƙudirin da ɗaukacin mamabobin majalisar suka albarkanta, ya tanadi tura sojojin zuwa tsakiya da kuma kudancin ƙasar ta somaliya da suke fi fama da rikici. Kana zai ƙaara kaso kudin da ƙasashen duniya ke kashewa domin samar da tsaro a ƙasar ta Somaliya. A Gobe ne dai idan Allah ya kaimu za a gudanar da taron ƙoli game da makomar ƙasar ta Somaliya a birnin London na Birtaniya. Tuni dai ƙungiyar agaji ta ƙasa da ƙasa wato Oxfam ta yi kira ga mahalarta taron da su bayar da fifiko ga batutuwan jin kai, maimakon na tsaro da kuma yadda za shawo fashin jiragen ruwa a tekun Aden.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Yahouza Sadissou Madobi