Somaliya: An kashe fitaccen dan jarida
February 17, 2020A kasar Somaliya, wasu da ake zargin mayakan kungiyar nan ta al-Shabaab ne sun hallaka wani fitaccen dan jaridan kasar mai suna Abdiwali Ali Hassan. Mayakan dauke da makamai sun bude masa wuta a yayin da ya ke hanyarsa ta komawa gida kamar yadda wasu shedun gani da ido suka tabbatar wa manema labarai.
Hassan na aiki ne da reshen wata kafar talabijin ta Universal mai hedkwata a birnin Landan da kuma wani gidan rediyo mai zaman kansa a kasar ta Somaliya kafin mutuwarsa. Mutumin dai shi ne dan jarida na farko da ya rasa ransa a wannan shekarar ta 2020 a hannun mayakan masu tayar da kayar baya.
Kasar da ke yankin kusurwar Afrika na daya daga cikin kasashen duniya da aikin jarida ya fi fuskantar barazana. 'Yan jarida kimanin tara ne suka rasa rayukansu a hannun mayakan a shekarar 2017 kamar yadda hukumar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International ta sheda.