Somaliya: Mutane 18 sun mutu
June 15, 2017Talla
Fafatawar da ta dauke su tsawon dare, ta kai ga asarar rayukan fararen hula 18 yayin da wasu sama da 30 suka ji raunuka. Lamarin dai ya samo asali ne lokacin da wani dan kunar bakin wake da kuma wani dauke da bindiga suka afkawa gidan abincin 'Posh Treats' a wannan Laraba.
Dan kunar bakin waken dai ya tashi Bam dinsa ne a mashigar gidan, yayin da shi kuwa dayan ya buda wuta kan sauran ya ayyu hannasu. Shaidu sun ce Sojoji sun ceto wadanda maharan suka tsare a gidan na abinci.
Kungiyar ta Al Shabaab da tuni ta dauki alhakin kai harin dai na ci gaba da haddasa asarar rayukan dubban jama'a a jerin hare-haren da ta ke kadadamarwa cikin kasar Somaliya da kuma wasu kasashe makwabtanta.