1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Somaliya ta sallami manyan jami'an tsaro

October 29, 2017

Gwamnatin kasar Somaliya ta kori wasu manyan jami'an tsaron kasar bayan tsanantar kaddamar da hare-hare da kasar ke fuskanta.

https://p.dw.com/p/2mh1p
Somalia Mehrere Tote bei Anschlag mit zwei Fahrzeugbomben in Mogadischu
Hoto: picture-alliance/AP Photo/F. Abdi Warsameh

Gwamnatin kasar Somaliya ta kori wasu manyan jami'an tsaron kasar bayan tsanantar kaddamar da hare-hare da kasar ke fuskanta. Manyan jami'an da aka sallama dai sun hada da shugaban rundunar 'yan sandan kasar Abdullahi Mohammad Ali da kuma na hukumar 'yan sandan ciki, Janar Abdulhakim Sa'id.

Sallamar wadannan jagororin na tsaro na zuwa ne bayan kawo karshen kawanyar da mayakan al Shabaab suka yi wa wani Otel da suka kai wa hari a jiya Asabar. Harin na bam dai ya kai ga mutuwar mutane akalla 27, kamar yadda sabbin alkaluma suka nunar. Bayanai sun ce an kashe mayakan na al Shabaab su uku tare da kame wasu uku. Harin dai na zuwa ne makonni biyu da kaddamar da wani mai muni da ya kashe rayuka sama da 350.