1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Somaliya: Tsaffin mayaka sun yi nadama

Abdullahi Tanko Bala
October 10, 2017

Wasu tsoffin mayakan kungiyar Al-Shabaab sun ce sun yi nadamar shiga cikin kungiyar inda suka ce an yaudare su ne da sunan yaki domin Allah don kafa daular musulunci a kasar.

https://p.dw.com/p/2laWJ
Somalia Kämpfer der al-Shabaab in Mogadischu
Mayakan kungiyar Al-Shabaab na SomaliyaHoto: M:Abdiwahab/AFP/Getty Image

Abu da Gardere ba sunaye ne na gaskiya ba. An yi amfani da su ne domin sakaye sunayensu na ainihi. Mutanen biyu dai wadanda ada suka kasance cikin mayakan kungiyar Al-Shabaab mai alaka da Al Qa'ida sun yi nadamar shiga cikin kungiyar. Gardere wanda shekarunsa sun haura 50 yana da mata biyu da 'ya'ya takwas kuma tsohon malamin makaranta ne. Da yake bada labarinsa ya ce ya shiga kungiyar ta masu tsattsaurar akida ce a shekarar 2008 lokacin da sojojin Habasha suka jagoranci farmakin yaki da ta'addanci a Somaliya. Mutanen biyu sun amince da yunkurin tashar Deutsche Welle na tattaunawa da su.Kuma ba tare da wani nuna shayi ba Gardere ya yi bayani:

Idan mutun bai cika yin lissafi ba, to zai yi nadama

Somalia Soldat 22.02.2014 Mogadischu
Sojojin Somaliya da ke yakar 'yan ta'addaHoto: Mohamed Abdiwahab/AFP/Getty Images

" Muna son daular Musulunci. Al-Shabaab na muradin rusa tsarin tarayya na federaliyya da dukkan wasu dabi'u na yammacin Turai tare da maye gurbin su da tsari na kalmar Allah. Wannan shi ne dalili kuma abin da ya ja ra'ayi na, na shiga kungiyar."

Sai dai ko da aka tambaye shi, shin Musulumci ya yi umarni a rika harba bam akan mutanen da basu ji ba basu gani ba?. A nan Gardere ya yi turus ya sunkuyar da kansa kasa sannan yace:

" Tarzomar kai hare-hare ita ce ta sa muka bar kungiyar. Mun so mu yi yaki da kafirai wadanda suka mamaye kasar musulunci. To amma ba haka suke yi ba. A yau kungiyar tana kashe jama'a fararen hula, su harba bam a kasuwanni, ba za mu goyi bayan wannan ba."

Bisa ga kalaman Gardere ya bar kungiyar 'yan gwagwarmayar kafa daular Musuluncin a shekarar 2016 bayan tsawon shekaru takwas Al-Shabab na aikata ta'asar ta'addanci da hare-hare a Somaliya da kasashe makwabta kamar Kenya da Uganda wadanda suka bada gudunmawar sojoji a hadakar rundunar kungiyar gamayyar Afrika AU domin yaki da Al-Shabaab. Amma shin ko me ya sa Gardere ya zauna tsawon wannan lokaci a cikin kungiyar?

'Yan ta'adda na saurin canza tunanin masu karamin karfi

Somalia al-Shabaab Kämpfer
Lokacin da 'yan ta'addan Somaliya ke faraitiHoto: picture alliance/AP Photo/M. Sheikh Nor

" Tarukan bita ake yi mana inda suke yi mana bayani kan akida tare da hujjoji domin jawo ra'ayin mu kuma ana yin wannan ne akai-akai yau da gobe, suna kuma sanar da mu cewa za a cimma nasara da yarda Allah, mun yi imani da haka da kuma yakinin samun kyakkyawar makoma a gaba, a saboda haka muka ci gaba da hakuri, to amma lamarin bai sauya ba."

Shi ma Abu ya yi imani da yan gwagwarmayar ta Islama. Ya shiga kungiyar Al-Shabaab kamar yadda ya ce a shekarar 2011. A lokacin ana fama da fari a Somaliya kuma yunwa ta tsananta. Mutane fiye da dubu 250,000 suka rasu a lokacin yawancin su sakamakon cutar kwalara. Ya ce Albashinsa a matsayin malamin makaranta ba ya isar sa tare da iyalina, sannan dalili na biyu kuma yawancin matasa a kauyensu sun shiga kungiyar.

Al-Shabaab Kämpfer in Somalia
Mayaka sun tattara mata da yaraHoto: Getty Images/AFP/M. Abdiwahab

"Na yi aikin karbar haraji, Al-Sahab sun sanya jama'a biyan harajin kasa, mutum zai biya nasa da na 'ya'yansa idan kuma za ka tura 'ya'yan ka makaranta za ka biya dala biyar a kowane wata."

Abu ya ce bai ji dadi ba domin kuwa bai amfana da komai ba a kungiyar. Shekarunsa 45 yana kuma da yaya hudu. Shima dai ya jima kafin ya bar kungiyar a shekarar 2015. Somaliya dai na daya daga cikin kasashe goma wadanda suka yi kaurin suna wajen ayyukan ta'addanci a duniya kamar yadda alkaluman kididdiga na kasa da kasa kan ta'addanci ya nunar. Tsakanin shekarun 2006 da 2015 mutane kusan dubu 4000 aka hallaka a hare haren ta'addanci a kasar.