Somaliya za ta dau fansa kan al-Shabaab
March 2, 2019Talla
Ikirarin gwamnatin na zuwa ne bayan wani mumunan harin kunar bakin wake da ya yi sanadiyar rayuka akalla 20 tare da jikkata wasu sama da 100. Kungiyar Al-Shabaab ta dau alhakin kai harin, sojojin Somaliya sun yi nasarar kashe hudu daga cikin maharan yayin da wasu suka tsere da raunuka.
A shekara ta 2010 kungiyar Al-Shabaab ta yi ikirarin hadewa da Al-Qaida domin cimma burin kawar da gwamnatin Somaliya, ganin yadda take da yawan mayaka akalla dubu biyar zuwa dubu tara abinda ya basu damar mamaye yankunan tsakiyar Somaliya da kudancin kasar a shekarun baya, sai dai sojojin kawancen kungiyar tarayyar Afirka sun yi nasarar kwace yankunan da suke iko da su.