1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Somaliya za ta raba fararen hula da makamai

August 14, 2014

Gwamnatin Somaliya ta kaddamar da shirin kwace makamai daga hannu mutane a wani mataki na magance ayyukan 'yan bindiga.

https://p.dw.com/p/1Cv16
Hoto: picture-alliance/dpa

Gwamnatin Somaliya ta kaddamar da sabon shirin karbar makamai daga hannu mutane, tare da samun nasarar karbe makamai kimanin 5000. Lamarin ya haifar da musayar wuta a birnin Mogadishu fadar gwamnatin kasar. Jami'ai sun kaddamar da aikin kafin makamai su shiga hannu mayakan wadanda suke da dangantaka da al-Qaeda.

Dakarun sun caje gidan wani jami'an soji da aka samu makamai da ake zargin za a sayar wa 'yan al-Shabaab. Tuni aka kama jami'in. Kasuwar sayar da makamai ta yi kaurin suna a kasar ta Somaliya wadda shugabannin kabilu ke tafiyarwa tun cikin shekarun 1990.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal