Ko kun san tabarbarewar tarbiyya da watsi da al'adu kan kawo lalacewar matasa su shiga wasu miyagin dabi'u da kuma ka iya shafar zamantakewar al'umma? Dangane da haka ma'aikatar kula da al'adu ta Jamhuriyar Nijar ta dauki matakin dakile wannan matsala. Shirin Taba Ka Lashe na wannan lokaci ya yi nazari kan matakan.