Al'adar Tarkama guda ce daga cikin al'adun da wasu matsafa a Jamhuriyar Nijar ke mutuntawa a yankuna da dama. Cike take da saddabaru baya ga abubuwan mamaki da al'ummomin yankunan ke imani da su. Duk da cewa tana fama da kalubalan sakamakon yaduwar addinin Islama, 'yan gado masu riko da al'adu dai na rike da ita.