1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

tabarbarewar tsaro a Somaliya

March 21, 2007
https://p.dw.com/p/BuP7

Mutane a kalla 14 ne suka rasa rayukan su a Somalia. Hakan ya faru ne bayan wani dauki ba dadi daya wanzu, a tsakanin yan fadan sari ka noke da kuma jami´an tsaro a birnin Magadishu.

Rahotanni dai sun tabbatar da cewa wannan arangama ta baya bayan nan ta faru ne a kusa da gidan gwamnatin kasar, inda yan sari ka noken ke kwanton baunan kaiwa jami´an tsaron na kasar hare hare.

Jim kadan dai da wannan arangama, yan fadan sari ka noken suka dinga jan gawarwakin sojojin da suka halaka akan titunan birnin.

A dai watan disambar bara ne, gwamnatin kasar tare da hadin gwiwar dakarun sojin Habasha suka fatattaki yan tawayen kasar daga birnin na Magadishu.