1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taimakawa wadanda rikicin Borno ya ritsa da su

Uwais Abubakar Idris
March 27, 2018

Gamaiyar kungiyoyin farar hula sun gudanar da zama na musamman a Abuja kan hanyoyin da za'a bi na samar da mafita daga mawuyacin hali da mutanen da rikicin ya ritsa da su, musamman a jihar Borno..

https://p.dw.com/p/2v4Jh
Nigeria Ausgabe von Nahrungsmitteln durch Hilfsorganisation
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Wannan sabon yunkuri da ake gudanar da shi a karkashin inuwar kungiyar Ingo Forum wacce ke aiki na sa ido a kan aiyyukan da kungiyoyi 36 na farar hula da ke aikin kai talafi ga mutane milya, da rikicin ya badala masu rayuwarsu a yankin arewa maso gabashin Najeriya, kokari ne na rarabe aya da tsakuwa, da ma hada karfi wuri guda domin cike gibin da ake fuskanta na kudi da kayan aiki.

Domin manufa ta kyautata hanzarin kai dauki ta hanyar taimako ga miliyoyin alummar yankin Arewa maso Gabashin Najeriya ya zama babban kalubale da ke bukatar taron dangi, abinda ya sanya tsara shirin nasu a karakshin kungiyar Mercy Corps. Roisin Mangam ita ce mai kula da dubarun tsare-tsare wadda ta bayyana man kalubalen da ke a gabansu:

Nigeria Kinder an einer Wasserstelle
Hoto: imago/ZUMA Press/Gilbertson

"Babban kalubale shine gagarumin bukatar  samar da taimakon agaji domin muna da mutane milyan 1.6 da suka rasa muhallansu wasu suna a sansanonin wasu makale a gidajen yan uwansu, ga yara milyan 3 da basa zuwa makaranta, baya ga mutane milyan uku da ke fuskantar rashin abinci. Wannan babban matsala ce, alal misalai a bara muna da bukatar dalla bilyan 1.5 amma mun samu dala 740, a bana ma muna neman dalla bilyan daya da rabi, abin taklaici bukatar tafi kudin da ake das u, muna da gibi, amma mun samu cima abubuwa da yawa dad an abinda muke da shi".

Duk da kokari na matsin lamba a ka  samar da tsaro ga fararen hula da samun Karin kudin gudarawa a fanin kai dauki ga mutanen da suke hannu rabana suna neman taimako saboda hali na tagayyara da wannan gamaiyar kungiyoyin ke yi, a dai dai lokacin da ake batun komawa gida ga mutanen da suka rasa muhallansu bisa radin kansu. Amma ga Farfesa Umar Pate yace akwai buktara sanin zahirin halin da yankin ke ciki.

Nigeria Boko Haram Anschlag in Maiduguri
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Ola

A lokutan baya dai gwamnatin jihar Bornon ta yi kokari na tsaftace tsarin kungiyoyi masu zaman kansu da ke aiki a jihar saboda zargin na ci da gumin mutanen da matsalar ta shafa, abinda ake wannan yunkuri yake kokari na tsarkake lamarin. Ko mecece illar rashin kaiwa ga mutanen da ke bukatar ga karancin kudin gudanar da ayyukansu? Mr Stanley Bantu na cikin wannan tafiya.

Abin jira a gani shine tasirin wannan kokari da manyan kungiyoyin talafawa irinsu Action Aid da Oxfam da ma Danish Refugee ta kasar Denmark musamman wajen  matsin lamba na samun kudadden kai dauki ga yankin Arewa maso Gabas da ake bukatar dalla biliyan 1.5 amma a bara aka samu dala milyan 700, abinda ke haifar da cikas ga taimakawa mutane miliyan 3 da ke fuskantar hatsari na rasa abincin agaji a yankin da ke sanya su fuskantar afkawa cikin hali na tagayyara.