1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taimakon dakile karuwanci a Najeriya

December 20, 2017

Shiga karuwanci a tsakanin yara mata da ke gararanba kan tituna birnin Abuja na Najeriya matsala ce da ke ruruwa tamkar wutar daji Naomi Jacob matashiya ce a Najeriya da ta tashi haikan wajen yaki da wannan matsala.

https://p.dw.com/p/2ph2V
Tanzania commercial sex workers
Hoto: Kizito Makoye

Naomi Jacob matashiya ce da bata wuce shekaru 25 a Abuja wacce yanzu haka ta tashi haikam wajen fafutukar dakile matsalar yawaitar karuwanci a tsakanin yara mata a karkashin cibiyar CEPEN  a inda tace shigar yara mata karuwanci na tayar mata da hankali tare da tunanin irin makomar da matan za su iya samu a nan gaba.

Mun fara wannan fafutukar shekaru 4 da mutane biyar masu kundumbala dubu 50 mun gudanar da shirye-shirye da bitoci masu yawa kuma mun sami nasasrori wajen daidaita halayyar matan da suka tsinci kansu a wannan matsalar, wani lokaci za ka ga matan na korafin ba su da ayyuka ba su da abinci da matsuguni gami da rashin samun mafadi, to amma duk da wadannan muna kokarin ganin mun magance wasu daga cikin matsalolinsu,.

Wannan  Jennifar Lukas ce wacce take taka muhimmiyar rawa wajen fafutukar kawar da karuwanci a tsakanin mata  anata bangaren nuni take cewar.

Yanzu haka dai matashiyar ta yi tsayin daka wajen ganin koda ba a kawar da kauwaancin ba to zai ragu matika a inda tayi nisa wajen samun nasara akan wadanda suka tuba tare da sauya hanyar rayuwa ta mutunci.