1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taiwan: An rantsar da sabuwar shugaban kasa

Zainab Mohammed AbubakarMay 20, 2016

Tsai Ing-wen ta kasance mace ta farko da aka rantsar a matsayin shugaban kasar Taiwan da ke fama da kalubalen tattalin arziki saboda rashin fitar da haja zuwa ketare.

https://p.dw.com/p/1Iqz4
Taiwan Tsai Ing-wens Amtsantritt
Hoto: picture-alliance/EPA/R. B. Tongo

Hawan ta kan kujerar shugabanci ya sake maido da jam'iyyar fafutukar demokaradiyya ta Progressive Party jan akalar lamuran kasar, tsaka-tsakin zaman doya da manja da Beijing.

Tsai ta sha rantsuwar karbar mulki ne a harabar fadar shugaban kasa da ke birnin Taipei gaban tutar kasar da hoton Sun Yat-sen, wanda ya kafa Jamhuriyar China amma ya yi kaura zuwa Taiwan a shekarata 1949, lokacin da 'yan kwammunisanci suka kwace mulkin Chinan.Shugaba Tsai dai na fuskantar kalubalen tattalin arziki da ya durkushe sakamakon rashin fitar da haja daka kasar, kasancewa babu mabukatu.