1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar ta soke shigar da mai Mali

Salissou Boukari RGB
September 27, 2022

Hukumomin Nijar sun soke shigar da man fetir zuwa Mali a sakamakon sabuwar takaddamar da ta kunno kai a tsakanin kasashen da ke makwabta da juna.

https://p.dw.com/p/4HQ4n
New York | Abdoulaye Maiga, Premierminister von Mali | UN-Generalversammlung
Hoto: Mary Altaffer/AP/picture alliance

Kalaman da Firaministan kasar ta Mali mai rikon kwarya Kanar Abdoulaye Maiga ya yi kan Shugaba Mohamed Bazoum, kalamai ne da suka haifar da dambarwa a shafukan sada zumunta na zamani a tsakanin 'yan kasashen biyu, daga bisani wata takarda da ta shafi batun hana ficewa da mai daga Nijar zuwa Mali na kokarin saka rudani cikin lamarin duk kuwa da cewa takardar an sanya mata hannu ne tun a ranan 21 na wannan watan Satumbar, inda ma wasu 'yan kasar ta Nijar ke kira da a zuba wa zukata ruwan sanyi.

Ita dai wannan takarda mai dauke da sa hannun shugaban Custom na kasa Kanal Harouna Abdallah, duk da cewa an sa mata hannu tun a ranar 21 ga wannan wata, kwanaki uku kafin jawabin firaministan kasar ta Mali a zauren taron Majalisar Dinkin Duniya ta ce, an soke bada izinin ficewa da mai zuwa kasar Mali idan dai ba na dakarun MINUSMA ba ne. Amma tuni wasu 'yan kasar suka soma danganta wannan takarda da lamarin da ya wakana na tankiya a tsakanin kasashen biyu.

Deutschland l Besuch des Nigerianischen Präsidenten in Berlin
Shugaba Mohamed Bazoum na NijarHoto: Presse- und Kommunikationsdienst der Präsidentschaft von Niger

Amma da yake magana kan wannan batu, Abdourahamane Bio, jami’in kula da hulda da jama’a a kamfanin kula da harkokin mai na kasa na SONIDEP, ya ce, kasar Mali dai na sayan mai daga kasashe kaman Nijar da Najeriya da sauransu wanda kuma ya kan biyowa ta Nijar din da sunan transit ya fice zuwa Mali amma kuma sannu a hankali aka gano cewa man na fadawa ga mugun hannu kaman na yan ta’adda.

Masu sharhi kan al’amuran tsaro irin su Ahmed Tarnane da ke bibiyar lamuran da ke wakana a yankin yammacin kasar ta Nijar da ma gabashi, ya ce, salon da 'yan ta’adda suka dauka na karbar kudade da kuma a hannun masu motoci ne ya sanya daukan wannan mataki daga hukumomin na Nijar.

Wannan batu na cece-kuce da ya kunno kai a tsakanin hukumomin na mali da na Nijar duk kuwa da cewa a hakumance Nijar din ba ta ce kala ba, amma kuma 'yan kasa kusan kowa na tofa na shi albarkacin baki kan lamarin. Sai dai da yake magana, dan majalisar dokoki Kalla Moutari kuma tsohon ministan tsaro na jamhuriyar Nijar ya ce, lamarin gaskiya ya bayar da mamaki.

Tun daga shugaban majalisar dokoki, zuwa ga wasu shugabannin kungiyoyin fararan hula irin su Nouhou Arzika zuwa Malamai ke yin kira da a zuba wa zukata ruwa tare da nesanta kai da furta miyagun kalamai zuwa wannan ko waccan kasa, domin Nijar da Mali dan juma da dan Juma'i da ke da makiyi daya, wato 'yan ta’adda da ke tayar da zaune tsaye.