1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tallafawa 'yan gudun hijirar kasar Mali

Salissou BoukariApril 17, 2016

Amirka ta sanar da bada wani tallafi na dala miliyan 29 domin taimaka wa 'yan gudun hijirar kasar Mali da a halin yanzu suke warwatse a kasashe daban-daban.

https://p.dw.com/p/1IXOb
Flüchtlinge aus Mali im Flüchtlingslager Djibo in Burkina Faso
'Yan gudun hijiran Mali a Burkina FasoHoto: Guy Lankester

A kalla 'yan kasar ta Mali dubu 145 ne suka bar matsugunnansu inda wasu ke a kasar Burkina Faso, wasu a Mauritaniya, wasu a Nijar yayin da wasu dubu 52 ke a wasu yankunan na kasar ta Mali. Sanarwar ta gwamnatin Amirka ta ce wadannan kudade za su taimaka wa kungiyoyin Majalisar Dinkin Duniya masu kula da 'yan gudun hijiran kamar su UNHCR da Hukumar Abinci ta Duniya da wasu kungiyoyin kasa da kasa da ke kasashen na Burkina Faso da Mauritaniya da Nijar da kuma Mali wadanda ke kula da 'yan gudun hijira. Kasar ta Amirka dai na fatan ganin komai ya daidaita a yankin arewacin kasar ta Mali ta yadda kowa zai samu komawa a cikin gidansa.