Nijar: Tallafi ta shafukan sada zumnta
November 1, 2022Wani abu da ke zaman mai alfanu ga marasa galihun a yanzu haka a Jamhuriyar Nijar, shi ne yadda suke amfani da kafofin na sada zumunta na zamani wajen aikawa da sakon neman taimako ga al'umma a duk lokacin da wani nasu ko su da kansu ke cikin bukatar hakan. Tallafin dai ya hdar da na rashin lafiya ko wani iftala'i har ma da neman agjin kayan daki ga yaransu mata. Sai dai kuma hukumomin kasar sun nunar da cewa, su ma a nasu bangaren suna bayar da tallafin, inda yara 'ya'yan marasa karfi ke samun agaji daga mahukuntan wadanda ke daukar dawainiyar lalurar da ta shafi asibiti. Mahukuntan dai na yin kira ga al'umma da su daina yin gajen hakuri wajen kai kokensu kafafen sada zumuntar. Koda yake wannan sabuwar hanyar na dada tasiri sosai wajen tallafawa mabukata, amma wasu na da ra'ayin cewa ba komai ya kamata a tallata duniya ta gani ba. Wasu kuma na da ra'ayin cewa, a kan samu 'yan damfara da ke amfani da batun neman agajin domin cimma wata bukata tasu ko kuma amfani da mara lafiyar koda kuwa ya ko ta samu sauki.