1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amsoshin Takardunku 10-07-23

Usman Shehu Usman AH
July 10, 2023

Birnin Damagaram, wanda ya kasance babban birnin Nijar daga 1911 zuwa 1926, ya ci gajiyar matsayinsa na mashigar hanyoyin sadarwa tsakanin sahara da Najeriya. Birnin ya kafu da babbar mnasarautar da ta yi dogon zamani.

https://p.dw.com/p/4TgQv
Hoto: Gazali Abdou Tasawa/DW

Hakika asalin sarautar ya kasance kusan 1736 kuma wuraren zama na sarakunan sun canza zuwa 1812. A wannan shekara ce Sultan Suleymane Dan Tanimoune ya kafa kujerar sarauta a Zinder sannan kuma a Birni. An ce an gina fadar ne a zamanin mulkin Tanimoune shahararren sarkin musulmi kuma wanda ya kafa daular Damagaram tsakanin 1850 zuwa 1852.