Shugaban INEC Farfesa Mahmood Yakubu
March 25, 2019An haifi Farfesa Mahmood Yakubu a shekarar 1962 a jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabashin Tarayyar Najeriya kuma ya yi karatunsa ne na firamare a makarantar firamare ta Kobi da ke cikin garin na Bauchi daga bisani kuma sai ya tafi kwalejin horas da malamai da ke garin Toro a jihar ta Bauchi dai inda nan ne ya kamala karatunsa na sakandare. Ta fuskar karatun jami’a kuwa, Farfesa Yakubu ya yi karatunsa na digirin farko a jami’ar Shehu Usmanu Danfodio da ke jihar Sokoto a arewa maso gabashin Najeriya din inda ya karanta ilimin tarihi.
Farfesa Mahmood Yakubu ya kuma yi karatunsa na digiri na biyu a Kwalejin Wolfson da ke Cambridge a Birtaniya inda ya karanci ilimin hulda kasa da kasa inda ya kamala a shekarar 1987. Ya kuma yi digirnsa na uku a a fannin tarihin Najeriya a Jami’a Oxford da ke Birtaniya inda ya kammala a shekarar 1991.
Ta fuskar aiki kuwa, Farfesa Mahmood Yakubu ya shafe tsawon lokaci yana koyarwa a kwalejin horas da sojojin Najeriya da ke Kaduna inda yake ware wajen koyar da dabaru na dakile yakin sari-ka-noke da kuma abubuwan da suka danganci tarihi da huldar kasa da kasa.
Farfesa Yakubu ya rike mukamin mukaddashin sakataren kudi da mulki na taron kasa da aka yi a tarayyar Najeriya a shekarar 2014, kuma daga bisani wato a watan Oktoban shekarar 2015 ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada shi a matsayin shugaban hukumar zabe mai zaman kanta wato INEC.