Afirka da Turai na Taro
February 17, 2022Talla
Shugaban kasashen Turai na nahiyar Afirka sun hadu a wannan Alhamis domin fara taron kwanaki biyu na kungiyoyin nahiyoyin biyu, kan bunkasa zuba jari, yayin da Turai ke fuskantar gasa daga kasashen China da Rasha a nahiyar Afirka. An dan samu tsamin danganta tsakanin Turai da Afirka bisa samar da riga-kafin annaobar cutar coronavirus zuwa nahiyar Afirka gami da fadada da ake samu na sojojin haya na Rasha a rikice-rikicen da suke faruwa a nahiyar Afirka.
Shugaba Macky Sall na Senegal wanda yake rike da shugabancin karba-karba na shugabannin kasashen Afirka ya ce burin Afirka yayin taron da Turai shi ne fadada dangantaka tsakanin bangarorin biyu ta yadda Afirka za ta iya samun ci-gaban zamani da take bukata.