Taron G5 Sahel kan tsaro a Burkina
February 5, 2019Talla
A wata sanarwar bayan taro da kasashen biyar mafi talauci a duniya suka wallafa, shugabannin kungiyar ta G5 sun bukaci samun hulda madaidaiciya da Majalisar Dinkin Duniya suna masu fatan ganin MDD ta dauki dawainiyar rundunar sojan kasashen.
Duk da rashin isassun kudade, kasashen na G5 Sahel sun ambata a wannan Talatar cewar za su ci gaba da yaki da ta'addanci tare da farfado da wasu hanyoyin kyautata jin dadin rayuwar jama'a da tattalin arziki, duba da yadda talauci ke taka muhimmiyar rawa wajen tursasa wasu jama'a a cikin migayun dabi'u.
Sai dai taron shugabanin na zuwa ne a daidai lokacin da ko a Litinin ma mayakan jihadi dauke da makamai sun hallaka wasu fararen hula 14 a wasu garuruwan Burkina Faso a iyaka da Mali.