1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Rikice-rikiceUkraine

Taron kasashe aminan Ukraine a Jamus

Abdullahi Tanko Bala
January 9, 2025

Kasashe aminan Ukraine na kokarin hanzarta samar wa kasar karin tallafi kafin Trump ya karbi ragamar mulki. Truimp dai ya sha sukar rawar da Amurka ke takawa a rikicin.

https://p.dw.com/p/4ozmx
Taron kolin kasashe aminan Ukraine a Ramstein
Taron kolin kasashe aminan Ukraine a RamsteinHoto: Heiko Becker/REUTERS

Muhimmin batu a taron kolin shugabannin shi ne karfafa makaman kariyar sararin samaniya domin fatattakar sojojin Rasha daga birane da iyakokin turai kamar yadda Zelenskyy ya wallafa a shafin sada zumunta na X gabanin taron.

Taron dai na kasancewa na karshe gabanin zababben shugaban Amurka Donald Trump ya karbi ragamar mulki a ranar 20 ga watan Janairu.

Makasudin taron shi ne domin hanzarta samar wa Kiev karin tallafi saboda Trump ya nuna cewa ba lallai ba ne ya ci gaba da tallafa wa Ukraine kamar yadda shugaba Joe Biden ya yi.

Firaministan Italiya Giorgia Meloni ta ce dukkan aminan kasashe suna fata Trump ya daidaita diflomasiyya da barazanar da ya ke yi a hannu guda, kada ya ce zai yi watsi da Ukraine.