Taron ƙasashen duniya domin taimakawa Somaliya wajan tabata da zaman lafiya
May 22, 2010Wakilai na gwamnatoci da shugabannin ƙasashen 55 na ƙasashen Afirka da yanki Asiya, da na Turai haɗe da mayan ƙungiyoyi na duniya da ke yin taro a birnin Istambul ,sun jadada aniyarsu ta kawo ɗauki ga hallartaciya gwamnati riƙon kwarya ta ƙasar Somaliya
Da ya ke jawabi a wajan bude taron sakataren majalisar dinkin duniya Ban Ki-moon, ya ce babbar hanyar da za ta zama ma fi a-Ala wajan sake dawo da kwanciyar hankali a ƙasar ta Somaliya, ita ce ta taimakawa gwamnatin akan yunƙurinta na sake sasanta tsakanin al-umar ƙasar, tare da yin yaƙi da yan aware .
Gwamnatin dai ta ƙasar Somaliya wace ke da taƙaitacen iko da birnin Mogadishio, na kan hanyar ƙara samu agajin ƙasashen duniya wajan sake kwato ƙasar daga hannu masu fafatikar kishin adinin islama
Mawallafi :Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohame abubakar