Tashin bam a Somaliya
October 4, 2011Wani harin bam da aka ƙaddamar cikin wata mota a tsakiyar Mogadishu, babban birnin ƙasar somaliya ya janyo mutuwar aƙalla mutane 57, tare da raunata wasu 30. Jami'ai sun kuma bayyana cewar akwai wasu 34 da ba a san makomar su ba ya zuwa yanzu, kuma akwai yiwuwar adadin mamatan ya ƙaru. Wani jami'in ƙungiyar tarayyar Afirka ta AU, wanda tunda farko ya ce adadin mamatan ya kai 50, ya bayyana cewar an ajiye motar ce a gaban harabar ma'aikatar kula da harkokin ilimi ta ƙasar Somaliya yayin da bam ɗin ya tashi. Jim kaɗan bayan tarwatsewar bam ɗin ne kuma ƙungiyar al-Shabab a ƙasar ta Somaliya, wadda ke da alaƙa da ƙungiyar alQaeda ta ɗauki alhakin tayar da shi. Dama dai ƙungiyar ta al-Shabab ta bayyana ƙaddamar da yaƙi da gwamnatin wucin gadin ƙasar Somaliya, wadda ke samun goyon bayan Majalisar Ɗinkin Duniya tun cikin tsawon shekaru masu yawa.
Mawallafi: Saleh Umar Saleh
Edita : Yahouza Sadissou