Tashin hankalin Somaliya
August 24, 2010A yayin da faɗa ke ƙara yaɗuwa a ƙasar Somaliya, ko da ayau ma ƙungiyar Alshabab dake ɗauke da makamai ta ɗauki alhakin kai hari a wani hotel, kuma harin ya hallaka mutane aƙalla 31 ciki har yan majalisar dokoki shida.
A tsakanin jiya da yau faɗanda dakarun gwamnati marar madafun iko da kuma ƙungiyar tsagerun Alshabab, ya hallaka mutane kimanin 60. Ministan yaɗa labarai Somaliya, yace 'yan ƙunar baƙin waken sun yi shiga irin ta jami'an tsaron gwamnati, suka saje har suka shiga cikin hotel ɗin, kuma babu ɓata lokaci suka yi ta buɗe wuta, da kuma anfani da ababen pacewa kamar gurneti. Wakilin DW a Mugadisho Abdi Nur, ya ziyarci Hotel ɗin ga kuma abinda yake cewa.
"Yanzu komai ya lafa a inda aka kai harin, jami'an tsaron gwamnati sun yiwa Hotel ɗin ƙawanya. Kuma suna hana mutane gittawa ta yankin baki ɗaya"
Shaidun gani da ido sukace sai dai kawunan mutane kawai ake ganin suna warwatse. Kuma sunga lokacin da aka harbi biyu daga cikin waɗanda suka kai harin, yayin da ɗayansu ya tada bama bamai dake jikinsa. Ministan yaɗa labaran ƙasar Adirrahim Omar Osman yace wannan harin ya tabbatar da rashin imanin da ƙungiyar Alshabab ke da shi. Wakilin DW yace a duk tsawon yinin yau ana jin tashin rokoki da bindigo cikin birnin Mugadisho.
"Faɗa dai bata ƙare ba, domin ina jin tashin manyan makamai, musamman a kuɗancin birnin. Buɗe wuta dai bai lafa ba, to amma bai kai yadda ya yi ƙamari a sifiyar yau ba"
Dama dai tun a jiya ƙungiyar Alshaba tace za ta ƙaddamar da hari, don kawar da sojin kiyaye zaman lafiya dake a Mugadisho. To sai dai kakakin ruddunar kiyaye zaman lafiya ta AU dake Somaliya, yace waɗanan hare-hare ba sabon abu bane.
"Tashin hankalin da muka gani a sa'o'i 24 da suka gabata, dama abune da muke tsammani. Dama cikin shiri muke. mun saba ganin haka a duk lokacin azumin watan Ramadan. Tun shekaru uku da muke nanan, a duk lokacin da Ramadan yazo, faɗa sai ta ƙaru. Kuma wannan baya nasaba da ƙarin sojojin kiyaye zaman lafiya. sam, domin dakarunma da aka ce za su zo, ba su iso ba, amma idan har sun zo, za mu faɗawa duniya"
Ƙungiyar kare haƙƙin mutanen dake fiskantar barazana, tace kimanin mutane dubu ɗaya suka rasa rayukansu a ƙasar Somaliya, tun daga watan junairu bana izuwa yau. haka an raunata a ƙalla mutane fiye da dubu biyu da dari takwas, aksari fararen hula. Ƙungiyar tarayyar Afirka dai ta ɗauki alƙawari tura ƙarin dakaru dubu biyu, don ƙarfafa tsaron guruwar gwamnatin Somaliya dake samun goyon bayan ƙasashen yamma.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Ahmadu Tijjani Lawal