Tattaunawa da sojojin RSP masu juyin mulki a Burkina Faso
September 22, 2015A halin yanzu dai ana ci gaba da tattaunawa da sojojin da suka yi juyin mulki na RSP kan su ajiye makammansu ba tare da an zubar da jini ba. Rahotanni na cewa, Shugaban kasar na rikon kwarya Michel Kafando ya samu mafaka a ofishin jakadancin kasar Faransa, sannan kuma sojojin sun sallamo Firaminista Laptanan Kanal Isaac Zida da safiyar wannan Talata inda ya koma gidansa na mulki, yayin da a hannu daya kasar Faransa cikin kakkausar murya ta nemi da masu juyin mulkin da su ajiye makammansu.
A wannan Talatar ce dai ake sa ran kungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS za ta yi wani zama na musamman a birnin Abuja na Tarayyar Najeriya domin duba wannan lamari duk kuwa da cewa kafin nan ba'a san abun da zai biyo bayan tattaunawar sojojin ba.