Tattaunawar sulhu a Somaliya
September 4, 2011Dakarun wanzar da zaman lafiya na ƙungiyar Tarayyar Afirka sun zagaye wurin da za'a yi taro domin tabbatar da tsaro.
Ɗaya daga cikin muhimman batutuwan da za su tattauna shine ƙarshen wa'adin mulkin da ke ci a ƙasar na tsawon shekaru bakwai yanzu, wanda ya gaza cimma buƙatun ƙasar na sulhu tsakanin ɓangarorin da ke gaba da juna, ƙirƙiro da sabon kundin tsarin mulkin ƙasar da kuma gudanar da zaɓe. Tattaunawar za ta sami halartar wakilai daga yankin Putland wadda ta ɓalle da ma sauran yankunan da ke kewaye da ƙasar. To sai dai babu wakilai daga Somaliland wadda ta ɓalle a 1991 da ma ƙungiyar tawaye ta al-shabab wacce ta ƙaurace daga Mogadishu zuwa kudancin ƙasar. Somalia ta kasance a cikin wani yanayi na yaƙin basasa tun bayan da aka hamɓarar da tsohon shugaba Mohamed Said Bare shekaru 20 da suka gabata. Duk yunƙurin ƙasashen ƙetare na kafa gwamnati mai ƙarfi a tsakiya ya ci tura, domin kawo yanzu, gwamnatin riƙon ƙwaryar ƙasar ta yi shugabanin ƙasa biyu da Fraim Minista biyar tun bayan kafa ta a shekarar 2004.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu
Edita: Abdullahi tanko Bala