1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsauni ya fada kan gidajen jama'a a China

June 24, 2017

Jami'an agaji a kasar China, na ci gaba da aikin neman ceton mutane a lardin Sichuan na kasar, inda zaftarewar kasa ta binne gidaje akalla 65.

https://p.dw.com/p/2fJIA
China Erdrutsch
Hoto: Picture alliance/Zumapress/He Qinghai

Jami'an agaji a kasar ta China sun ce sama da rayukan mutane 100 ake fargabar sun salwanta cikin lamarin. Wata tashar talabijin a kasar ta ruwaito cewar wani tsauni ne ya fada kan rukunin gidajen jama'a, bayan wani ruwan sama mai karfi da aka yi a lardin.

Masu aikin ceto kimanin dubu guda ke aikin neman wadanda lamarin ya ritsa da su. Bala'in ya shafi gidaje akalla 65 inda kalilan ne aka kaiga ceto ya zuwa ranar Asabar.

Matsalar zaftarewar kasa dai ba sabuwar aba ba ce a wasu yankunan kasar China, musamman bayan samun ruwan sama mai girma. Ko a cikin watan Janairun bana ma dai wasu mutane 12 sun mutu a lardin Hubei, lokacin da kasa ta fada kan wani Otel a yankin.