1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsohon shugaban Burkina Faso ya nufi Marokko daga Cote d'Ivoire

Mohammad Nasiru AwalNovember 20, 2014

Tsohon shugaban na Burkina Faso Blaise Compaore da kanshi ya yanke shawarar yin kaura zuwa Marokko da ke arewacin Afirka.

https://p.dw.com/p/1DqkY
Burkina Faso Ex-Präsident Compaore Archiv 2011
Hoto: picture alliance/AP Photo/R. Blackwell

Wani kakakin gwamnatin Cote d'Ivoire ya ce tsohon shugaban kasar Burkina Faso Blaise Compaore wanda aka tilasta masa sauka daga kan karagar mulki biyo bayan wani bore, ya bar mafakarsa ta wucin gadi da ke Cote d'Ivoire, kuma ya doshi kasar Marokko inda zai yi kaura. Bruno Kone kakakin gwamnatin Cote d'Ivoire ya fada wa kamfanin dillancin labarun Reuters cewa Compaore wanda ya kwashe shekaru da yawa a kan kujerar shugabancin Burkina Faso, ya yanke shawarar sauya mafakarsa zuwa Marokko. Kakakin ya kara da cewa a kullum kofofin kasarsa a bude suke ga Blaise Compaore.