Tsugune ba ta kare ba a Somaliya.
June 7, 2013Kwamitin tsaro na Majalisar Dinki Duniya, ya yi garagadin cewa har yanzu kungiyar masu kaifin kishin addini ta Al'shabab, na ci gaba da kawo tarnaki da kuma barazana ga shirin tabbatar da zaman lafiya a Somaliya, duk kuwa da cigaban da ake samu a baya bayannan na inganta yanayin tsaro a kasar.
A wata sanarwa da kwamitin ya fitar wadda baki dayan mambobi 15 da ke cikin sa suka amince da ita, sun bukaci gwamnatin Somaliya da ta hukunta duk wani wanda yake da hannu wajen take hakkin dan Adam, da ya hadar da muzgunawa kananan yara da kuma fyade da ga bangaren 'yan tawaye ko kuma dakarun gwamnati, da akayi a kan wadanda suka warwatsu ta hanyar tserewa daga gidajensu yayin yaki da aka kwashe shekaru da dama ana gawabzawa a kasar.
Tun daga shekara ta 1991 kawo yanzu, babu wata tsayayyiyar gwamnati a Somaliya biyo bayan juyin mulki da aka yiwa tsohon shugaban gwamnatin kama karya, da ya kwashe shekaru da dama ya na mulki a kasar kafin daga bisani kuma yaki ya barke wanda ya dai-dai ta kasar dake yankin kahon Afirka.
Rahotanni sun bayyana cewa duk da dakarun wanzar da zaman lafiya na Afirka sun samu nasarar korar 'yan tawayen Al-Shabab daga Somaliyan, har yanzu 'yan Al-shabab din na kokarin ganin sun ci gaba da tada zaune tsaye tare kuma da kashe fararen hula.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe