EU na zargin Rasha da cutar da Alexei Navalny
April 19, 2021Babban jami'in hulda da kasashen ketare na kungiyar ta EU Josep Borrell ya sanar a wannan Litinin cewa Turai za ta kama Rasha da laifin duk abin da ya faru da dan adawar. Wannan na zuwa ne a yayin da a dazu da safe Rasha ta sanar da cewa ta kai Alexei Navalny asibiti, tana mai cewa shi ne a radin kansa ya amince da a kai sa asibitin.
Makonni uku ke nan dai da Alexei Navalny ya daina cin abinci a gidan kason da hukumomin Rasha ke tsare da shi, kuma likitansa ya ce lafiyar jagoran adawan na Rasha ta tabarbare, zai iya mutuwa a kowane lokaci idan ba a dauki wani mataki ba.
Sai dai kungiyar Tarayyar Turai na ci gaba da yi wa Rasha barazana a kan lamarin, amma Rashan ta musanta gallaza wa dan adawar, ta kuma yi ikirarin yin ramuwar gayya idan har Turai ta kuskura ta sanya mata karin wasu takunkumi a kan lamarin.