SiyasaTurai
Turai za ta kai Turkiyya kotu kan hakkin dan Adam
December 3, 2021Talla
Majalisar ta Turai ta zargi Turkiyya da watsi da hukuncin kotun Turai na 2019 da ya bukaci Turkiyyar ta saki Kavala tun da ba a kama sa da wani laifi a hukumance ba. Sai dai gwamnatin Turkiyya ta gargadi majalisar Turan da cewa wannan yunkuri ne na yi mata shisshigi kan harkokinta na cikin gida.
Tun a shekara ta 2017 ne dai gwamnatin Turkiyya ta kama Osman Kavala bisa zargin sa da hannu a wata zanga-zangar kin jinin gwamnati da aka yi a shekara ta 2013. Kazalika gwamnatin Shugaba Erdogan na zargin Kavala da bayar da gudunmawa wurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a shekara ta 2016.